Читать бесплатно книгу «Wani Neman Jarumai » Моргана Райс полностью онлайн — MyBook
image
cover

WANI NEMAN JARUMAI

LITTAFI NA DAYA A JEREN ZOBEN MAI SIHIRI

MORGAN RICE


Bayani a kan Morgan Rice


Morgan Rice shine na daya a cikin marubuta da suka fi ciniki daya rubuta LABARAIN MAYU, wani jere na matasa daya kunshi lattafai goma sha daya (kuma kirgen bai saya ba tukuna); mafi cinikin jeren littatafan RAYUWAN ABUBUWA UKU, wani labarin hangen duniyar wata rana daya kunshi littatafai biyu (kuma kirgen bai saya ba tukuna); da kuma mafi cinikin na kololuwar jeren littatafan fantasi na ZOBEN MAI SIHIRI, mai littatafai goma sha uku (kuma kirgen bai kare ba tukuna).


A kan samu littatafan morgan a wallafe a takarda da kuma a karance da murya, kuma akwai tarjaman littatafain a harsunan jamus, faransa, italia, sipania, potugal, japanawa, sin, swedanawa, hollandia, turkiya, hungariya, cek da silovaniawa (wasu yarukan suna biyo wa a baya).


Morgan na da son yaji daga wurinka, saboda haka ka hanzarta ka ziyarci adireshinsa na yanar gizo a www.morganricebooks.com domin shiga jerin wasikun email, kasamu kyautan littafi, kasamu wasu kyaututuka na musamman, ka sauke na’urar wayoyi kyauta, kasamu labarai da dumiduminsu, ka sada zumunci a facebook da twitter kuma ka kasance kana sadarwa a koyaushe.

Zabbabun yabo wa Morgan Rice


“Fantasi mai ruhun kansa da yake hada yanayin gaibu da mamaki a cikin jigon labarinsa. Wani Neman Jarumai ya kasance a kan muradi da cika burin rayuwa wanda ya kaiwa ga girma, dattakum, birgewa….. Ga masu son labarin fantasi mai sokar tonetone, mabiya, na’urori, da kuma tsari suna bada wadansu shiryayyun haduwa da suke kewayuwa a kan yanayin rayuwan Thor. Daga tashinsa a matsayin dan yaro mai buri zuwa zama matashi mai fuskantan hadururuka da yawa amma ya rayu…. Farko ne na abinda zai zama kololuwar jere wa matasa.

Sharhin Littatafai na Yamma ta sakiya (D.Donovan, mai sharhin littafi irin na yanar gizo).


“ZOBEN MAI SIHIRI yanada dukan mahadan samun nasaran kwassam: kullekulle, akan kullekulle, al’ajabi, marasa soron bardawa, da soyayya masu ginuwa amma cike da ciwon zuciyoyi, yaudara da cin amana. Zai nishadantar da kai na sa’o I, kuma ya biya wa yara da manya bukata. An shawarci duk masu karatun fantasi su kasance dashi a dakin litafaffansu.”

--Sharhin litattafai da finafinai, Roberto Mattos


“Littafin Rice mai kolouwar nishadantarwa a shasin fantasi [ZOBEN MAI SIHIRI] ya kunshi duka alamomi na sashin – yanayi mai karfi, da samun karfin gwiwa daga sohuwar sukotlan da tarihinsa, da kuma kyakyawan fahimtan shiga da fita na gidajen sarauta.

---Sharhin Kirkus


“Naso yanda Morgan Rice ya gina yanayin Thor da duniyan da yake zaune cikinta. Yanayin kasan da halittun da suke yawo sun samu kwatance mai kyau… naji dadin [yanayin]. Yayi gajarta ya kumayi dadi…shauran kananan yanayin sunyi daidai saboda haka ban rikice ba. Akwai yawon zuciya da lokutan tsoro, amma shirin da aka yi a ciki bai wuce gona da iriba. Littafin zai yi wa matashin mai karatu daidai…mafarin abubuwa masu muhimmanci shine akwai…”

Sharhin Littatafai na San Francisco


“Acikin wannan littafin farko na kololuwar fantasin jeren zoben mai sihiri mai cike da daga iri iri (wanda ya kai littatafai goma sha hudu a yanzun), Rice yana nunawa masu karatu dan shekaru goma sha hudu Thorgrin “Thor” McLeod, wanda burinsa a rayuwa shine ya samu shiga rundunan Silver, zababun mayaka da suke yiwa sarki hidima….. Rubutun Rice ya hadu kuma yanayin na nishadantarwa.”

Jaridan Mawallafa na sati sati


“[WANI NEMAN JARUMAI] ya kasance littafi mai karantuwa da sauri kuma cikin sauki. Karshen surorin na samaka sha’awan cigaba da karatu ba tare da ka ajiye litaffin ba. Akwai abubuwan da ba a rasawa a littafin amma wannan bai rage mata armashi ba. Karshen littafin yasa ni son na samu littafi na gaba da sauri kuma haka din nayi. Ana iya sayan dukkan jeren littatafen zoben mai shiri guda tara a shagon kindle na Amazon kuma wani neman jarumai ya kasance kyauta a yanzu domin ka fara! Idon kana neman karatu mai sauri wanda ya kuma kasance da dadin karatu idan kana hutu wannan littafin zai maka sosai.”

kantin yanar gizo na FantasyOnline .net

Wasu littatafan da morgan rice ya wallafa


ZOBEN MAI SIHIRI

WANI NEMAN JARUMAI (LITTAFI NA DAYA)

PARETIN SARAKUNA (LITTAFI NA BIYU)

KADARAN SU (LITTAFI NA UKU)

KUKAR MAI GASKIYA (LITTAFI NA HUDU)

RANTSUWAN CIKAN BURI (LITTAFI NA BIYAR)

RATAYAN KOKARI A BAKIN DAGA (LITTAFI NA SHIDA)

BORIN TAKWUBA (LITTAFI NA BAKWAI)

YARDAN MAKAMAI (LITTAFI NA TAKWAS)

SAMAN DARIN SIHIRAI (LITTAFI NA TARA)

KOGIN ABUBUWAN KARIYA (LITTAFI NA GOMA

MULKIN BAKIN KARFE (LITTAFI NA GOMA SHA DAYA)

KASAR WUTA (LITTAFI NA GOMA SHA BIYU)

MULKIN SU SARAUNIYAI (LITTAFI NA GOMA SHA UKU)

RANTSUWAN YAN’UWA (LITTAFI NA GOMA SHA HUDU)


RAYUWAN ABUBUWA UKU

FILIN DAGA NA DAYA: MASU SHANYA BAYI A RANA (LITTAFI NA DAYA)

FILIN DAGA NA BIYU (LITTAFI NA BIYU)


LABARUN MAYU

AJUYE (LITTAFI NA DAYA)

SOYYAYE (LITTAFI NA BIYU)

WANDA A KA CI WA AMANA (LITTAFI NA UKU)

KADDARARE (LITTAFI NA HUDU)

BUKATACCE (LITTAFI NA BIYAR)

AURARRIYA (LITTAFI NA SHIDA)

RANTSATSE (LITTAFI NA BAKWAI)

SAMMAME (LITTAFI NA TAKWAS)

TARYAYYE (LITTAFI NA TARA)

BUKATTATE (LITTAFI NA GOMA)

KADDARRARE (LITTAFI NA GOMA SHA DAYA)



Ka saurari jeren littafin ZOBEN MAI SIHIRI a karance!

kariyar aikin fasaha a shekara 2012 na Morgan Rice.


Duka yanci na kyebe. Sadai Kaman yanda dokar kariyar aikin fasaha ta Amerika ta 1976 ta bada izini, an hana buga wannan wallafafiyar aikin ta kowane hanya, ko ajiye ta a ma’ajiyin fasaha ba tare da izinin mawallafin ba.


Anyi wa wannan littafin lasisin amfani dashi domin jin dadin kanka ne kawai. Ba a yadda ka sayar dashi ko ka badashi kyauta ba. Idon zaka so ka raba shi da wani, yi hakuri ka sayi wani wa kowane mai karantawa. Idon kana karatun wannan littafin ba tare da ka saya bane, kokuma ba a saya domin amfaninka bane, yi hakuri ka mayar sai ka sayi naka. Nagode maka saboda baiwa aikin da wannan mawallafin yayi tukuru muhimmanci.


Wannan labari ne irin na tasuniya. Sunaye, yanayi, sanao’i, kungiyoyi, wurare, abubuwan dasuka auku dukansu sun kasance tunanin marubuci ko labarin tasuniya. Kama da wani mutum araye ko mace da zasuyi sosayine.


Hoton bayan marfin littafi kareriyar aikin fasaha na razoom game, anyi anfani dashi a karkashin lasisin Shutterstock.com.


ABIN DA KE CIKI

SURA NA DAYA

SURA NA BIYU

SURA NA UKU

SURA NA HUDU

SURA NA BIYAR

SURA NA SHIDA

SURA NA BAKWAI

SURA NA TAKWAS

SURA NA TARA

SURA NA GOMA

SURA NA GOMA SHA DAYA

SURA NA GOMA SHA BIYU

SURA NA GOMA SHA UKU

SURA NA GOMA SHA HUDU

SURA NA GOMA SHA BIYAR

SURA NA GOMA SHA SHIDA

SURA NA GOMA SHA BAKWAI

SURA NA GOMA SHA TAKWAS

SURA NA GOMA SHA TARA

SURA NA ASHIRIN

SURA NA ASHIRIN DA DAYA

SURA NA ASHIRIN DA BIYU

SURA NA ASHIRIN DA UKU

SURA NA ASHIRIN DA HUDU

SURA NA ASHIRIN DA BIYAR

SURA NA ASHIRIN DA SHIDA

SURA NA ASHIRIN DA BAKWAI

SURA NA ASHIRIN DA TAKWAS

“kan da yasa hulan sarauta baya samun sauki”

--William Shakespeare

A Littafin Henry IV, Shashi na biyu

SURA NA DAYA

Yaron ya tsaya a kan kololuwar karamar tudun kasar da take kasa kasa a masarautar yamma na zoben, ya kalli arewa, yana kallon farkon tasowan rana. A iya nisan kallonsa, yana ganin koren shinfidaddun tudu, wayanda suna sauka su haura kaman tozon rakumi a cikin wadansu kwari da ganiyan tudu. Hasken bullowan ranar farko mai launin ruwan lemu ya dan dade yana haskawa a kan rabar safe, yana sa su kyalli, yana ara wa hasken, majigin da yayi dede da yadda yaron yake ji a ran sa. Yaron bai cika tashi da wuri haka ba kuma bai taba nisan kiwo daga gida haka ba – kuma bai taba haurawa tudun da tsawo haka ba – domin yasan yin hakan zai jawo fushin mahaifinsa. Amma a wanan ranar, bai damu ba. A wannan ranar, yayi biris da miliyoyin dokoki da ayyuka masu yi masa danniya na tsohon shekaru goma sha hudu. Hakan ya faru ne saboda wannan ranan na daban ne. Rana ne da ya kasance kaddararsa ta iso.

Yaron, Thorgrin na masarautar yammacin daular yan dangin McLeod na kudu – sananne ga duk wadanda yaso da suna Thor kawai – dan auta cikin yara maza hudu, mafi karacin soyuwa a wurin mahaifinsa, ya kwana idonsa biyu saboda begen wannan rana. Yayi ta juye-juye, da idanu cike da ruwa, yana jira, yana fatan farkon tasowan rana. Saboda rana kamar haka yakan faru ne sau daya a cikin shekaru da yawa, kuma in har ya bar zarafin ya kubuce masa, zai makale a wannan kauyen, yakuma dawwama a aikin kula da garkunan mahaifinsa har iya rayuwarsa. Wannan kuma ya zama tunanin da ba zai iya hakuri da shi ba.

Ranar shiga soja . Ya kasance rana daya ne rak da sojojin sarki ke zaga wa duka dauloli suna zaban masu son shiga rundunan sarki. Tun da yake raye, Thor baya mafarkin komai face wannan. A wurin shi, ma’ anar rayuwa abu daya ne rak: shiga silver, zababbun hafsosin rundunar sarki, sanye da kayan adon yaki mafi kyau da kuma tattatun makamai a ko ina a cikin duka masarautai biyun. Kuma ba a shiga cikin silver sai mutum ya shiga babbar runduna, rundunonin masu koyan aikin tsaro da shekarun su ke sakanin goma sha hudu da goma sha tara. Kuma idon mutum bai kasance dan fittatun mutane ba, ko wani sanannen jarumi ba, to babu wata hanyar shiga babbar runduna.

Ranar shiga soja ne kawai ta sha banban, wannan abin ba safai ba, da ya ke faruwa a kowani shekara da rundunonin sarki ke raguwa kuma hafsosin sarki ke zaga kasan suna neman sabbobin dauka. Kowa ya san kalilan a ke daukawa a cikin yaku bayi – kuma musamman an san kadan ne daga ciki za su samu shiga babban runduna.

Thor ya karanci yanayin wuri sosai, yana dubawa ko zai ga wata alamar motsi. Yan silver, ya sani, ya zama dole su biyo nan, hanya makadaiciya zuwa kauyen sa, kuma yaso ya zama wanda zai fara ganin su. Garken tumakin sa na ta nuna rashin yarda a kewaye da shi, sun tada kukan haushi da murya daya kuma suna nuna su fa ya mayar dasu gangarar tudu, inda mafi kyawun ciyayi suke. Yayi kokarin ya toshe ihunsu, da kuma warinsu. Sai ya zama masa dole ya tara hankalinsa a guri guda.

Abinda yasa ya iya juran duka wannan, shekarun da yayi yana kiwo, yayi yana bauta wa mahaifinsa, yayi yana bauta wa yayunsa, yayi yana mai samun mafi karancin kulawa kuma mafi aikatuwa, shine zaton cewa watan watarana shi zai bar wannan wurin. Wata rana, idon yan silver sukazo, shi zai bawa duk wadanda suka raina masa mamaki da zabansa da za a yi. Farat daya shi zai dale amalankensu yayi bankwana da duk wannan damuwowin.

Mahaifin Thor, a kan huja, bai taba daukan shi da muhimmanci a matsayin dan takaran shiga rundunan tsaro ba – musamman ma, bai taba daukan shi a matsayin dan takaran komai ba. A madaddin haka, ya bada soyyayarsa da kulawa gabadaya wa yayun Thor su uku. Babban cikinsu dan shekaru goma sha tara ne kuma shauran sun bi juna da shekaru dadaya, wanda yasa Thor yazama kanin kowanne a cikin su da akalla shekaru uku masu kyau. Wata kila domin shekarunsu na kurkusa da juna kokuma watakila domin su sun yi kama da juna amma ba kama da Thor ba, su ukun a manne da juna suke a kowani lokaci, batare da sun nuna wani alaman sun san da rayuwar Thor ba.

Abinda yafi munima shine duk sun fishi tsayi da fadi dakuma karfi, shikuma Thor, duk da ya san shi ba gajere bane, Thor yaji cewa shi karami ne in an kwatanta dasu, yana raina ginannu kafafuwansa in ya kwatanta da nasu masu kama da manyan bishiyoyin gamji. Mahaifinsa bai dauki ko mataki saboda magance wannan ba – Kaman ma yana jin dadin haka ne – ya bar Thor ya dinga kiwon tumaki da wasa makamai alhalin yan’uwansa sunanan suna koyon yaki. Abinda ba a fada amma da kowa ya sani shine cewa, Thor zai karasa sauran rayunsa a dan kallo ne, zai tilasstu da kallon yan’uwansa suna yin abubuwan al’ajabi. Da mahaifinsa da yan’uwansa za su samu yadda suke so, da kaddarar sa zai zama, ya kasance a nan, a hadiye a cikin wannan kauyen, yana bawa iyalensa duk kular da suka nema a wurinsa.

Wani munin abin kuma shine cewa Thor ya fahimci cewa yan’uwansa, ta wata hanyan, suna jin shakkan shi, watakila ma sun tsane shi. Thor na iya ganin haka a kowane kalon su zuwa gare shi da yanayin su. Bai san ta yaya bane, amma yana tayar da wani abu, Kaman tsoro, kishi a cikin su. Watakila domin ya sha bambam dasu, bai yi kama dasu ba kokuma domin rashin magana da irin yanayin su; baya ma sa kaya kaman su, mahaifinsa yakan bar mafi kyawun komai – alkebbobi masu launin malmo da jaja, da makamai na manyan mayaka – wa yan’uwansa, alhali a kan bar Thor da sa matattun summokara.

Duk da haka, Thor yayi mafi kyawun amfani da dammar da yasamu, yana samo hanyoyin da siturorinsa za su yi daidai dashi, yana daura dogayen riguna da igiya akewaye da kugun sa, saikuma, yanzu rani ta iso, yakan yanka hanayen rigunan domin hanayensa da suka riga suka yi baki su sha iska. Rigarsa da yi daidai da mattatiyar wandon alawaryonsa – kayan mallakarsa guda biyu kacal – da takalmansa da a ka yi daga mafi talautuwan patar leda, sun kai ga har kwabrinsa. Ba a yi su da patar da tayi kokusa da wadda a kayi na yayunsa dashi ba, amma ya san yanda yake sasu amfanar shi. Ya kasance tamkar alamar makiyayin dabbobi ne.

Amma fa yana da wuya a ganshi a yanayin kowa. Thor na da sayi kuma tsiriri, da marikar yarda da kai, habban masu kirki, sayyayun kumatu da idanu masu launin toka, yana kama da jarumin da baya bata. Mikekiyar gashin kansa mai launin kasa sun zubo baya a jejjere a kansa, kasa kadan da kunnuwansa, sannan a bayan gashin, idannunsa na kyalli Kaman kifin tarfasa a cikin haske.

Za a bar yan’uwan Thor suyi bacci a wannan safiyar, a basu lafiyayen abinci, kuma a tura su zuwa wurin zaben mayaka da mafi kyawun makamai da kuma sa albarkan mahaifinsa – alhali ba a ma barin shi shima ya kasance. Ya taba kokarin tayar da maganan da mahaifinsa sau daya. Sakamakon hakan bai yi kyau ba. Mahainfinsa ya kasaita hirar a hanya na kawai, kuma bai sake gwada wa ba. Lamarin ya kasance ba adalci ne kawai.

Thor na da muradin kin kaddarar da babansa ya shirya masa. Daga ganin alamun farko na rundunar gidan sarauta, zai koma gida a guje, ya fuskanci mahaifinsa, kuma, koyaki koyaso, ya bayyanar da kansa wa mutanen sarki. Shima ma zaiyi takaran shiga rundunan mayaka da shauran. Mahaifinsa bai isa ya hana shi ba. Ya ji wani kulewa a cikin sa a yayin tunanin hakan.

Ranar farkon ya dan kara haurawa, sai a lokacin da na biyun, da launin koren minti, ya fara haurowa, yana kara wa sararin samaniya wani irin haske mai launin malmo, Thor ya hango su.

Ya mike a tsaye, gashi a mimmike, yana mamaki. A nan, daga can nesa, wani mafi karancin yanayin amalanken doki, tayun sa suna tada kura zuwa sama. Bugun zuciyarsa ta karu a yayin daya ga bullowar wata kuma; sai kuma wata. Daga nan ma yana ganin amalanku masu launin gwal suna kyalli a cikin rana, Kaman kifi mai bayan zinari dayaka tsalle ya koma ruwa.

A lokacin daya kirga har goma sha biyu a cikin su, ya gagara hakuri ya kara jira. Da duukan zuciya a cikin kirjinsa, da manta garken tumakinsa a karo na farko a rayuwarsa, Thor ya juya sai ya gungura kasan tudun da tsauri, da muradin yin koma mai zata bukata domin bayanar da kansa.

*

...
8

Бесплатно

0 
(0 оценок)

Читать книгу: «Wani Neman Jarumai »

Установите приложение, чтобы читать эту книгу бесплатно

На этой странице вы можете прочитать онлайн книгу «Wani Neman Jarumai », автора Моргана Райс. Данная книга имеет возрастное ограничение 16+, относится к жанрам: «Зарубежное фэнтези», «Героическое фэнтези». Произведение затрагивает такие темы, как «эпическое фэнтези», «волшебные миры». Книга «Wani Neman Jarumai » была издана в 2019 году. Приятного чтения!